Home Labaru Badakalar NDDC: Kakakin Majalisa Ya Bukaci Minista Ya Bayyana Sunayen ‘Yan Majalisan...

Badakalar NDDC: Kakakin Majalisa Ya Bukaci Minista Ya Bayyana Sunayen ‘Yan Majalisan Da Aka Ba Kwangila

229
0

Kakakin Majalisar Wakila Femi Gbajabiamila, ya bai wa Ministan Ma’aikatar Yankin Naija Delta, Sanata Godswill Akpabio, sa’o’i 48 ya bayyana sunayen ‘yan majalisar da aka baiwa kwangiloli a Hukumar Raya Yankin Naija Delta tare da kuma bayanai dalla-dalla a kan kwangilolin.

Kakakin Majalisar ya ce matukar ministan ya kasa fitar da sunayen, majalisa za ta yi amfani da karfin ikon da doka ta tabbatar an gudanar da binciken.

Gbajabiamila ya bayyana hakan ne yayin zaman da suka yi a jiya Talata, kwana daya bayan da ministan ya yi zargin cewa, mafi yawan kwangilolin da hukumar NDDC ta bayar an bai wa ‘yan majalisa ne.

Yayin bayar da bahasi a gaban Kwamitin Kajalisa Wakilai akan NDDC a ranar Litinin, Sanata Akpabio ya yi ikirarin cewa ‘yan majalisa su ne suka fi amfana da kwangilolin NDDC.

Yanzu an zuba ido aga ko ministan zai bayyana sunayen ‘yan majalisar da ya yi ikirarin an basu kwangilolin kusan kashi 60 ciki 100, kafin wa’adin sa’o’i 48 da majalisar ta bashi.