Home Labaru Ta’addanci: ‘Yan Kungiyar Boko Haram Sun Kashe Ma’aikatan Agaji

Ta’addanci: ‘Yan Kungiyar Boko Haram Sun Kashe Ma’aikatan Agaji

272
0

Masu ikirarin Jihadi da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe ma’aikatan agajin da suka sace a arewa maso gabashin kasar nan.

Kungiyoyin agaji na Action against Hunger da International Rescue Committee sun tabbatar cewa ma’aikatan su na cikin wadanda aka kashe.

Wani bidiyo da aka fitar a watan jiya ya nuna ma’aikatan agajin da aka kama suna neman a ceto su.

Shugaban Muhammadu Buhari ya dora alhakin kisan kan kungiyar Boko Haram, inda kuma ya sha alwashin hukunta wadanda suka aikata kisan.

A nasu bangaren kungiyoyin bada agajin Action Against Hunger da International Rescue Committee sun nuna matukar kaduwar su akan  kisan ma’aikatan su.

Mayakan boko Haram sun sha far wa ma’aikatan agaji kuma sau da dama suna kashe su.