Home Labaru Sulhu: Olubadan Da Hakiman Sa Sun Tattauna

Sulhu: Olubadan Da Hakiman Sa Sun Tattauna

247
0

Manyan hakimai 21 da tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Abiola Ajimobi ya daukaka  matsayin su zuwa sarkuna a masarautar Ibadan sun yi zaman sulhu da Olubadan na Ibadan inda suka tattauna a kan takaddamar da ta haifar rabuwar su da zuwa kotu domin warware matsalar.

Takaddama a tsakanin Olubadan na Ibadan Oba Saliu Adetunji da manyan fadawan sa da hakimai 21 ta faro ne a watan Agustan shekarar 2017,  lokacin da tsohon Gwamnan Jihar Abiola Ajimobi, ya daukaka matsayin hakiman zuwa sarakuna  inda Olubadan ya ki amincewa da haka.

Tun daga wancan lokaci ne aka fara kiran wadannan sababbin sarakuna 21 da ‘Oba’ wato Sarki, inda suka rika sanya hular sarauta tare da kebe kansu daga halartar taron da Olubadan ya saba yi da su a fadar sa.

Hakan ya sa fadar Olubadan ta shiga karar daukaka darajar hakiman zuwa sarakuna a Babbar Kotun Ibadan wacce ta yanke hukuncin dakatar da sabbin sarakunan daga ci gaba da kiran kansu sarakuna.

An dai cigaba da takaddama tsakanin Olubadan da tsohon Gwamna Abiola Ajimobi, wanda ya daukaka kara zuwa kotun gaba tare da barazanar sauke Olubadan daga sarauta har zuwa lokacin da sabuwar gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Seyi Makinde, da ya dauki matakin tsame kansa daga shiga cikin takaddamar.