Home Labaru Nasara: Limaman Coci 5 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Ogun...

Nasara: Limaman Coci 5 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Ogun Sun Kubuta

358
0

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta sami nasarar kubutar da daukacin limaman cocin Ridim su biyar da aka yi garkuwa da su.

An dai fara kubutar da daya daga cikin limaman cocin ridim guda biyar da aka yi garkuwa da su a kan babbar hanyar nan ta Binin daga Shagamu.

Ibelegbo Chidinma wacce ita ce kadai mace a cikin manyan limaman cocin biyar da aka yi garkuwa da su ta samu kubuta ne ba tare da ko kwarzane a jikinta ba.

DSP Abimbola Oyeyemi, Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi ya ce izuwa yanzu rundunar na shirin kai matar cocin ta ridim da ke kan babbar hanyar nan ta Legas daga Ibadan a jihar Ogun.

Shugaban cocin ta ridim Fasto Adeboye ne ya sanar da rahoton garkuwa da manyan limaman cocin nasu a  inda ya ce an yi garkuwa da su ne a lokacin da suke kan hanyar su ta halartar taron limaman cocin daga Kudu maso Gabashi inda aka yi garkuwa da su akan hanyar Binin daga Shagamu a jihar Ogun.

Leave a Reply