Home Labaru Suka: Atiku Ya Yi Magana Kan Kamen Da Dss Ta Yi

Suka: Atiku Ya Yi Magana Kan Kamen Da Dss Ta Yi

250
0

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a babban zaben 2019 Atiku Abubakar ya yi Allah wadai ta kama wasu ;yan Najeriya biyu da ake zargin jami’an hukumar DSS kan yawan sukar gwamnati da su keyi.

Omoyele Sowore

Mutane biyun da aka kama dai sune Omoyele Sowore, dan gagwarmaya kuma mawallafi jaridar Sahara Reporters da kuma Abubakar Idris, malamin jami’a kuma dan Kwankwasiyya da ya dade yana sukar tsare-tsaren gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano da Shugaba Muhammadu Buhari.

Atiku ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa kudin tsarin mulkin kasa ya ba kowa damar fadin ra’ayin sa, kuma wannan shine ginshikin demokradiyar mu a Najeriya.

An kama Sowore ne a daren Juma’a a gidan sa da ke Legas kuma wani hadimin sa da suke tare ya ce jami’an SSS ne suka kama shi suka tafi da shi ofishin su da ke Shangisha a Legas.

A na zargin cewa wadannan mutanen jami’an tsaro ne da na hukumar DSS masu dauke da fararen kaya.