Home Labaru Sulhu: Gwamna Matawalle Ya Ce Da ‘Yan Bindiga Aka Tattauna Ba Da...

Sulhu: Gwamna Matawalle Ya Ce Da ‘Yan Bindiga Aka Tattauna Ba Da Boko Haram Ba

125
0

Gwamna Matawalle na jihar Zamfara ya ce ba a a hannun Boko
Haram aka karɓo daliban makarantar sakandirin Kankara ba,
daga hannun ‘ƴan bindiga aka karbo su.

Gwamnan ya ce a zaman sulhun da aka yi da ‘yan bindigan
kafin amso yaran, sun gindaya wasu matsalolin da ke ci musu
tuwo a ƙwarya wanda kuma aka yi musu alkawarin za a sasanta.

Daga cikin ƙorafin da ‘yan bindugan suka yi sun ce akwai yadda
ake kashe musu shanu da cin zarafin su da suke zargin ƴan
banga ko ƙato da gora na yi.

Gwamna mutawalle ya ce a shirye ake a ci gaba da ƙoƙari irin
wannan wajen sulhu don tsare ƙasa, kuma duk wanda ya ƙi zai
fuskanci fushin hukuma.