Home Labaru Ceto Yara: Wasu ‘Yan Najeriya Na Bakin-Ciki — Hadimin Buhari

Ceto Yara: Wasu ‘Yan Najeriya Na Bakin-Ciki — Hadimin Buhari

102
0

Mai tamaka wa shugaban kasa kan harkokin sada zumunta,
Bashir Ahmed, ya yi zargin cewa wasu daga cikin ‘yan Najeriya
ba su ji daɗin ceto ɗaliban Ƙanƙara su 344 da aka yi ba.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce a lokacin
da aka sace yaran, wasu sun nuna farin cikin su a fili, a yanzu
kuma sun nuna baƙin cikin su a fili bayan ceto su.

Gwamnatin Katsina ta tabbatar da cewa duka yaran 344 da aka
ceto na cikin ƙoshin lafiya.

A baya dai an ta samun bambancin adadin ɗaliban da aka sace,
inda tun a farko aka ce sama da 600 aka sace.