Home Labaru Yaran Kankara: Shugaba Buhari Ya Ba Daliban Da Aka Ceto Shawara

Yaran Kankara: Shugaba Buhari Ya Ba Daliban Da Aka Ceto Shawara

283
0

Shugaban Muhammadu Buhari ya gana ɗaliban makarantar
Kankara a Katsina bayan kuɓutar da su daga ƴan bindigar da
suka sace su.

Shugaban kasan ya gana da ɗaliban ne a fadar gwamnatin
Katsina kwana guda bayan ceto ɗaliban su sama da 340.
An kubutar da ɗaliban da yawancin su yara ƙanana a ranar
Alhamis bayan shafe kusan mako ɗaya a daji a hannun masu
garkuwa da su.

Shugaba Buhari ya jinjinawa gwamnatin jihar Katsina da kuma
sauran waɗanda suka taimaka aka kuɓutar da ɗaliban.

Shugaban ya fara yin jawabin ne da yin kira ga ɗaliban su
saurare shi kuma su fahimce shi inda ya ce su ƙara himma ga
neman ilimi, su manta da abin da ya faru a baya.

Ya roki ‘yan Nijeriya su cigaba da hakuri da gwamnatin sa a
wannan lokaci da ta ke fama da matsalolin tsaro da tattalin arziki
da matsain rayuwar da mutane ke ciki.