Home Labaru Sulhu: Amurka Da Taliban Na Daf Da Kulla Yarjejeniya

Sulhu: Amurka Da Taliban Na Daf Da Kulla Yarjejeniya

254
0

Bayan an shafe watanni ana tattaunawa tsakanin ‘yan Taliban da Amurka, da alama kwalliya za ta biya kudin sabulu.

A wannan karon, ana ganin tattaunawar ta kai wani mataki da muhimmancinta zai iya kawo karshen yaki mafi muni da ya daidaita kasar.

Jakadan Amurka Zalmay Khalilzad a wallafa wani sakon Twitter, “idan ‘yan Taliban suka yi abin da ya dace, mu ma zamu yi namu kokarin domin cimma yarjejeniya.”

Wakilan kungiyar Taliban sun sanar da kafar yada labarai ta BBC cewa suna da karfin gwuiwa, amma da sauran aiki a gaba.

Karanta Labaru Masu Alaka: Ta Kacame Tsakanin Atiku Da Buhari A Kan Hana ‘Yan Siyasa Shiga Amurka

Sannan Taliban ta san Shugaba Trump na son mai da sojojin Amurka gida kafin zaben shugaban kasa da za a yi a badi.

Amma duk da sanin haka, Mista Khalilzad ya ci gaba da nanata cewa Amurka za ta janye ne kawai bayan an biya mata wasu bukatu.