Home Labaru Shugaba Buhari Ya Nemi A Kama Wadanda Su Ka Kashe Fasto

Shugaba Buhari Ya Nemi A Kama Wadanda Su Ka Kashe Fasto

207
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya aika da sakon ta’aziyya ga Mabiya darikar Katolika na addinin Kirista game da kisan babban Limamin cocin su Rabaren Paul Offu da aka yi.

Buhari ya aika da sakon ne a Ranar Asabar da ta gabata, kamar yadda mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Garba Shehu ya bayyana.

Ya ce Shugaba Buhari ya jajenta wa al’ummomi da gwamnatin jihar Enugu da iyalan marigayi Paul Offu.

 Buhari ya nuna fushin sa a kan yadda aka kashe babban limamin Cocin, don haka ya ba jami’an tsaro umurnin su shiga neman wadanda su ka aikata mummunan aikin don a hukunta su.

Garba Shehu ya bayyana cewa, shugaba Buhari ya ce gwamnatin sa za ta cigaba maganin masu tada kayar baya tare da kira ga jama’a su sa Nijeriya cikin addu’a a halin yanzu.