Home Labaru Sallar Layya: Raguna Sun Yi Tsada A Kaduna

Sallar Layya: Raguna Sun Yi Tsada A Kaduna

898
0

A jihar Kaduna farashin Raguna sun yi tashin gwaron zabi wanda ke tsorata masu siye, duk da cewar akwai Ragunan kamar a raba su a kyauta.

Wani bincike da kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya gudanar a Kaduna, ya nuna cewa kasuwanni sun cika makil da Ragunan, amma akwai karancin masu siye.

A kasuwar dabbobi dake Zango, kan titin Bashama, da kuma kasuwannin dabbobi dake Rigasa, akalla farashin Ragunan matsakaita ya na farawa ne daga naira dubu 40, sannan kuma manyan Raguna farashin su ya  fara ne daga naira dubu 95.

Karanta Labaru Masu Alaka: An Bukaci Musulmi Su Gu Ji Cin Bashi Domin Sayen Rago

Wasu masu siyan Ragunan sun bayyannawa manema labarai cewar farashin Ragunan ya yi sama sosai idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata, a lokacain da ke sayra da rago matsakaici akan kudi naira dubu 20 manya kuma naira dubu  85.

Wani da ya zo siyan rago a kasuwar Zango , mai suna Rayyanu Ibrahim, ya koka akan tsadar farashin Ragunan, amma ya ce yana sa ran farashin zai karye kafin ranar Salla.

Wani mai sayar da Ragunan, mai suna  Alhaji Musa Cikaji, da ke kasuwar dabbobin ta Rigasa, ya yi zargin tashin farashin ne a kan tsadar abincin dabbobin da tashin farashin jigilar su da kuma mawuyacin yanayin da tattalin arzikin kasa ke  ciki.