Home Labaru Karar Kwana: Tsawa Ta Halaka Mutane 7 A Garin Yola

Karar Kwana: Tsawa Ta Halaka Mutane 7 A Garin Yola

1670
0

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta tabbatar da mutuwar wasu mutane bakwai sanadiyar wata tsawa ta ta afku a birnin Yola.

Shugaban hukumar a jihohin Adamawa da Taraba Abani Garki, ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN a Yola.

Ya ce daga cikin yankunan da abun ya shafa sun kunshi     Runde Baru, da Wuro Jabbe, da Damilu, da Yolde Pate, da Bachure, da Kofare da kuma Jambutu, duk a kananan hukumomin Yola ta kudu da Yola ta arewa.

Abani Garki ya daura alhakin yawan ambaliyar ruwa da ake samu a yankunan kan sakacin mutanen garuruwan, cewa mazauna yankin suna kewaye filayen su da siyar da su ba tare da bin tsari yadda ya kamata ba.

Ya shawarci gwamnatin jihar Adamawa ta duba lamuran filaye sannan ta bukaci mutane su guji gini a yankunan ambaliyar ruwa.