Home Labarai Sufurin Jirgin Kasa: Sufurin Jirgin Kasa: Za’a Fara Jigila a Cikin Birnin...

Sufurin Jirgin Kasa: Sufurin Jirgin Kasa: Za’a Fara Jigila a Cikin Birnin Abuja – Minista

358
0

Gwamnatin tarayya tace nan gaba kadan Jirgin kasan da zai rika jigila a cikin Babban Birnin Tarayya Abuja domin rage wahalar zirga-zirga.


Ministan Abuja, Malam Muhammadu Bello ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara Kamfanin CCECC da ke kwagilar aikin jirgin.


A yayin ziyarar an zagaya da ministan da ayarinsa lungu da sako na cibiyar gudanar ayyuka da kuma sarrafa jirgin da ke Idu.


A jawabin Babban Sakataren Hukumar FCTA Mista Olusade Adesola ya ce, makasudin ziyarar shi ne, su duba inda aka kwana a aikin jirgin da kuma inda za a dora.


Adesola ya ce hukumar ta kashe kudi mai yawa, da kuma tallafin Gwamnatin Tarayya har an kai ga matakin soma gwajin jirgin kafin annobar COVID-19 ta bulla, lamarin da ya ta tilasta dakatar da aikin.


Dangane da batun tsaro, Babban sakataren yace an tanadin cikakken tsarin tsaro ga jirgin tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro na birnin.

Leave a Reply