Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa EFCC ta ce ba ta san inda Dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a jam’iyyar APC, Abdussaalam Abdulkarim (A.A. Zaura), ya shiga ba.
EFCC ta shaida hakan ne a gaban Babbar Kotun Jihar Kano, inda ake zarginsa da hannu wajen damfarar wani dan kasar Kuwait Dalar Amurka miliyar daya da dubu 300.
An dai shirya dawo da ci gaba da sauraron karar ce a ranar Litinin, bayan Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da umarnin sakinsa tare da sake shari’ar.
Lauyan dan siyasar, Ibrahim Waru, ya ce ba lallai sai wanda yake karewar ya bayyana a gaban kotun ba kasancewar sun shigar da wata karar suna kalubalantar hurumin kotun na sauraron karar.
Kazalika, ya ce wanda yake karewar ba shi da cikakkiyar lafiyar da zai iya tsayawa a gaban kotun, kuma suna da shaidar asibiti a kan hakan.
Daga bisani kotu ta dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Tun a watan Yunin 2020 ne dai wata kotun ta wanke A.A. Zaura tare da korar karar, lamarin da yasa EFCC ta sake daukaka kara domin neman a sake duba shari’ar.