Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tafi birnin Landan a yau litinin din nan domin a duba lafiyarsa.
Bayanin tafiyar yana kunshe ne a cikin wani sako da Kakakin shugaban, Femi Adesina ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce ana saran Buhari zai dawo gida Najeriya ne cikin mako na biyu a watan Nuwamba.
A baya dai shugaban ya sha tafiya Landan domin duba lafiyarsa tun lokacin da ya fara jagorantar kasar nan.
A 2017, Shugaban ya kwashe kwanaki 150 a Burtaniya a wata tafiyar duba lafiyar da ba a bayyana abin da ke damun sa ba.
Buhari ya kara komawa Burtaniya a watan Mayun 2018 domin ganin liktansa, inda ya yi kwana hudu kacal a kasar ta Burtaniya.
A watan Nuwambar 2020 ne, mai dakin shugaban kasar Aisha Buhari, ta ce akwai bukatar a inganta bangaren lafiyan Najeriya domin a rage tafiye-tafiyen neman magani kasashen waje.
You must log in to post a comment.