Home Labaru Sufuri: Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja Ya Taka Nakiya An Kuma Buɗe...

Sufuri: Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja Ya Taka Nakiya An Kuma Buɗe Masa Wuta

5
0
An kai wa wani jirgin ƙasa da ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja hare-hare har biyu, kamar yadda tsohon dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani ya bayyana.

An kai wa wani jirgin ƙasa da ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja hare-hare har biyu, kamar yadda tsohon dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani ya bayyana.

A wata wallafa da ya yi a shafin san a Twitter, Sanata Shehu Sani ya ce an kai hari a kan jirgin yamma na ranar Larabar da ta gabata, inda jirgin ya taka nakiya, sannan aka buɗe ma shi wuta a daidai saitin da direba ya ke da kuma tankin jirgin.

Ya ce an kuma sake kai hari a kan wani jirgin na safiyar Alhamis din nan kuma ya na daga cikin fasinjojin, inda ya taka nakiya ta fashe har ta lalata hanyar jirgin. Sanatan ya kara da cewa, ikon Allah ne kawai ya sa su ka tsira, inda ya sake wallafa wani bidiyon da ya nuna isar jirgin da ya ce ya na ciki na safiyar Alhamis a Abuja.