Home Labaru Banga: Dan Majalisa Ya Tsallake Rijiya Da Bayan Hannun Yan Daba A...

Banga: Dan Majalisa Ya Tsallake Rijiya Da Bayan Hannun Yan Daba A Majalisar Zamfara

6
0
Dan majalisar dokoki ta jihar Zamfara mai wakiltar mazabar Talata-Mafara ta Arewa Shamsudden Hassan ya tsallake rijiya da baya a zauren majalisar.

Dan majalisar dokoki ta jihar Zamfara mai wakiltar mazabar Talata-Mafara ta Arewa Shamsudden Hassan ya tsallake rijiya da baya a zauren majalisar.

Lamarin dai ya faru ne, yayin zaman tantance mutane biyu da gwamnan jihar ya gabatar da sunayen su domin tabbatar da su a matsayin kwamishanoni, sai dai Shamsudden Hassan ya nuna rashin goyon bayan sa a kan Hajiya Rabi Ibrahim Shinkafi, wadda ta taba rike mukamin mai ba gwamna Matawalle shawara.

Dan majalisar, ya ce ba ya goyon bayan nadin Hajiya Rabi matsayin a kwamishanan saboda gajiyayya ce, ya na mai cewa idan majalisar za ta tantance ta ne bisa ayyukan da ta yi a baya lallai ba za ta ketare ba.

Sai dai kafin ya kammala jawabin sa, wasu fusatattun matasa sun dira kan sa su na dura ma shi ashar tare da jifar sa, inda su ka ce ya yi shiru ko kuma ya dandana kudar sa.

Daraktan yada labarai na majalisar Mustafa Jafaru Kaura, ya ce ba su ji dadin abin da ‘yan barandar siyasar su ka yi ba, don haka daga yau majalisar ta yanke shawara haramta masu halartar duk wani zama da za ta yi nan gaba.