Gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 2 da miliyan 300 a cikin kasafin shekara ta 2022, domin a biya tsofaffin shugabanni kasa hakkokin su.
Wata majiya ta ce, rayayyun tsofaffin shugabannin farar hula da na soji ne za su amfana da kudaden.
Daga cikin wadanda za su amfana da kudin akwai Janar Yakubu Gowon, da Janar Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Janar Abdulsalami Abubakar.
Sauran sun hada da Ernest Shonekan da Janar Olusegun Obasanjo da kuma Goodluck Jonathan.