Home Labaru Sufeton ‘Yan Sanda Ya Bayar Da Umarnin Cafke Masu Sayar Da Sabbin...

Sufeton ‘Yan Sanda Ya Bayar Da Umarnin Cafke Masu Sayar Da Sabbin Kudi

25
0

Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Usman Alkali Baba, ya bada umarnin kama masu saida sabbin takardun kudi, inda ya ce a kama duk wadanda aka samu da hannu a lamarin.

Usman Alkali Baba, ya ce sun hada gwiwa da dukkan jami’an tsaro, domin sa kafar wando guda da duk wanda aka kama kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.

Wannan dai y,a na zuwa ne bayan umarnin da gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya bada, na hada gwiwa da jami’an hukumomin EFCC da ICPC domin kama masu yi wa tsarin sabbin kudin zagon kasa.

Tuni dai hukumomin EFCC da ICPC sun baza jami’an su a bankuna, domin sa ido a kan yadda ake hada-hadar sauya sabbin kudin.