Wani kasurgumin dan ta’adda Kachalla Balleri, ya ce sun dade su na amfani da sabbin kudden Naira da aka sauya wa fasali, hasalima da su su ke sayen makamai.
Kachalla Balleri dai ya na daya daga cikin jagororin ‘yan ta’adda da ake nema ruwa a jallo, wadanda su ke ta’addanci a wasu yankunan jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna da wasu sassan Jamhuriyar Nijar.
A cikin wani faifan bidiyo, an nuna shugaban ‘yan bindigar ya na baje kolin sabbin takardun kudin naira da aka sauya wa fasali.
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele, ya ce manufar sauya fasalin kudin ta kunshi dakile yadda masu garkuwa da mutane ke karbar kudin fansa, amma Kachalla Baleri ya ce manufar za ta azabtar da talakawa ne kawai, domin su ko a jikin su.
You must log in to post a comment.