Home Home Barazanar Kisa: Kotu Ta Sa A Cafke Shugaban APC Na Kano

Barazanar Kisa: Kotu Ta Sa A Cafke Shugaban APC Na Kano

31
0
Kotu ta bada umarnin a tsare Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano Abdullahi Abbas, tare da gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin barazanar kisa.

Kotu ta bada umarnin a tsare Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano Abdullahi Abbas, tare da gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargin barazanar kisa.

Babbar Kokotun tarayya da ke zama a Kano ce ta sa a tsare, a bincika a kuma gurfanar da Abdullahi Abbas, bisa zargin barazanar kisa, da tada zaune tsaye da kuma kalaman tsana ga Mahmoud Lamido.

Mahmoud Lamido ya shaida wa kotun ta bakin lauyan sa cewa, shugaban jam’iyyar ya kira shi a waya, ya na barazana ga rayuwar sa da cewa sai ya batar da shi.

Akalin kotun Mai Shari’a S.A Amobeda, ya dage sauraren karar zuwa ranar 16 ga wata Fabairun domin ‘yan sanda su aiwatar da umarnin kotu.