Gwamnatin mulkin soja ta Sudan ta damke jami’a hambararriyar gwamnatin Omar al-Bashir kuma sun yi alkawarin kyale masu zanga-zanga su ci gaba da boren da suke yi.
Wani kakakin gwamnatin ya kuma ce an mika wa kungiyoyin da suke shirya boren da su nada wanda suke so ya zama firai ministan gwamnatin riko da za a kafa.
Masu zanga-zangar dai sun sha alwashin ci gaba da nuna bacin ransu a bisa titunan biranen kasar har sai an mika mulki ga gwamnatin riko ta farar hula.
Har zuwa yau masu boren na ci gaba da mamaye ma’aikatar tsaron kasar da ke Khartoum.
A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta hannun kakakinta Manjo Janar Shams Ad-din Shanto, gwamnatin ta ce a shirye ta ke ta aiwatar da dukkan matakan da kungiyoyin ‘yan adawa da kungiyoyin fararen hula suka cimma matsaya a kai.
You must log in to post a comment.