Kasar New Zealand ta tura runduna ta musanman domin ‘yanto wata jami’ar lafiya ta kasar Louisa Akavi, da mayakan IS suka yi garkuwa da ita a Syria tun a shekarar 2013.
Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa wato Red Cross da ta ke yi wa aiki ta ce ta samu wasu bayanai da ke tabbatar ma ta da cewa jami’an yar shekaru 62 na nan da ranta.
An dai sace ma’aikaciyar lafiya tare da wasu direbobi biyu ‘yan Siriyan a yayin da ta ke aiki ne a shekarar 2013, sai dai tun wancan lokacin ba a kai ga samun isassun bayanai da za su taimaka don gano inda aka yi da wadannan mutanen ba.
Red Cross ta ce, manema labarai sun guji yada labarin garkuwa da ma’aikatan domin kada su jefa rayuwarsu cikin hadari.
A yau ne gwamnatin New Zealand ta sanar da tura runduna ta musamman don ‘yanto matar da kuma direbobin da aka ce har yanzu suna hannun IS.