Wata gobara ta kone shaguna akalla 35 bangaren ‘yan nama dake kasuwar Kurmi a jihar Kano.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara a jihar Kano, Saidu Mohammed, ya bayyana haka a lokacin yake magana da manema labarai a Kano.
Ya ce da misalin karfe 4:56 na safe ne, wani mutum mai suna Ado Musa, ya kira sanar da hukumar cewar gobara ta tashi a kasuwar, amma nan da nan jami’an hukumar kashe gobara, suka isa wajen da misalin karfe 5:03 domin hana wutar gobarar yaduwa zuwa sauran shaguna.
Mohammed, ya ba ‘yan kasuwar shawara su lura da kiyaye wa wajen amfani da duk wasu kayayyaki da kan iya haddasa gobara domin gudun sake samun afkuwar irin wannan hatsari.