Home Labaru Sudan: An Fara Yi Wa Omar Al-Bashir Shari’a Kan Juyin Mulkin Day...

Sudan: An Fara Yi Wa Omar Al-Bashir Shari’a Kan Juyin Mulkin Day A Yi

287
0
Al-Bashir Ya Ce Yariman Saudiyya Ne Ya Ba Su Kudin Da Aka Kama
Al-Bashir Ya Ce Yariman Saudiyya Ne Ya Ba Su Kudin Da Aka Kama

An fara yi wa Omar al-Bashir – tsohon shugaban Sudan – shari’a a babban birnin ƙasar Khartoum.

OMAR AL- BASHIR

Ana tuhumarsa ne game da juyin mulkin da ya ba shi damar hawa mulki a shekarar 1989.

Idan aka samu tsohon shugaban da laifi – wanda ya mulki Sudan tsawon shekara 30 – za a iya yanke masa hukuncin kisa.

Ita ma Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (International Criminal Court) ta zargi al-Bashir da aikata laifukan yaƙi da kisan ƙare-dangi a yankin Darfur da ke yammacin ƙasar.

A shekarar da ta gabata ne aka tumɓuke shi daga kan mulki bayan an shafe watanni ana zanga-zangar neman mulkin dimokuraɗiyya.

Leave a Reply