Home Coronavirus GesIllar COVID-19: Kungiyar EU Sun Amince Da Tara Yuro Biliyan 750 Don...

GesIllar COVID-19: Kungiyar EU Sun Amince Da Tara Yuro Biliyan 750 Don Gyara Tattalin Arzikinsu

174
0

Jagororin Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) sun amince da wani wani gagarumin shiri na tayar da komaɗar tattalin arzikinsu sakamakon durkushewar da cutar korona ta haifar.

EU

Ministocin na EU sun shafe kwana huɗu suna tattaunawa a Brussels, babban birnin ƙasar Belgium.

Manyan jami’an sun sake komawa teburin tattaunawa ne domin rattaba hannu kan yarjejeniyarr samar da tallafin yuro biliyan 750 domin bunƙasa tattalin arzikisu.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana lamarin a matsayin rana mai ɗumbin tarihi ga EU.

Wakilan kuma suna ƙara tattaunawa kan samar da kasafin kudi na tsawon shekara bakwai masu zuwa.