Home Labaru Kiwon Lafiya Iftila’i: Hukumomi Sun Yi Kashedi A Kan Ambaliya A Kano Da Makwabtanta

Iftila’i: Hukumomi Sun Yi Kashedi A Kan Ambaliya A Kano Da Makwabtanta

227
0
Kano: Babu Fita Ranakun Litinin, Talata, Alhamis Da Asabar — Ganduje
Kano: Babu Fita Ranakun Litinin, Talata, Alhamis Da Asabar — Ganduje

Hukumar  kula da yanayi ta kasa da ta kula da ayyukan bada agajin gaggawa suna fadakar da al’umar kasar nan game da matakan kaucewa ambaliyar ruwa.

Itama hukumar kula da koramun Hadejia da Jama’are ta ce ta yi tsare tsaren kubutar da gonakin manoma daga wannan annoba a yankunan jihohin Kano, Jigawa da kuma Bauchi.

AMBALIYAR RUWA A JIHAR KANO JIYA

Wani rahoto da hukumar kula da yanayi ta fitar a makon jiya, ya yi hasashen cewa, jumlar kananan hukumomi 102 ne daga cikin 774 na kasar nan , ka iya fuskantar ambaliyar ruwa a damanar bana.

Rahoton ya nuna a jihar Kano, kananan hukumomi 17 ne cikin 44 na jihar zasu iya fuskantar ambaliyar.

Kadan daga ciki sune Gwarzo, Kura, Warawa Wudil , Rimingado Nasarawa da kuma Kumbotso.

Dr. Kabiru Ibrahim Getso dake zaman kwamishinan muhalli na jihar Kano ya ce rahotan na hukumar kula da yanayi ya zaburar dasu wajen daukar matakan da suka dace.

Baya ga barazanar rusa muhalli, ambaliyar na lalata amfanin gona na biliyoyin naira a kowace shekara, al’amarin dake jefa manoma halin ni’yasu.