Home Labaru EFCC Ta Gabatar Da Wata Gagarumar Shaida A Kan Shehu Sani

EFCC Ta Gabatar Da Wata Gagarumar Shaida A Kan Shehu Sani

598
0
EFCC Ta Gabatar Da Wata Gagarumar Shaida A Kan Shehu Sani

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta ce ta samu faifan sautin muryar da ya zama shaidar ta a kan zargin da ta ke yi wa tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani.

Wata majiya ta ce, faifan muryoyin wadanda sun kai guda 13, su na kunshe ne da hirar Shehu Sani da Sani Dauda mamallakin kamfanin ASD Motors.

Hukumar EFCC, ta gabatar da faifan muryar ga tsohon sanatan a gaban lauyoyin sa Audu Mohammed Lawal da Glory Peter, inda Shehu Sani ya tabbatar da cewa muryar sa ce a faifan, amma ya yi zargin cewa an goge wasu sassan hirar da su ka yi.

Duk da Sanatan bai zargi hukumar EFCC da goge wasu sassa na hirar ba, amma ya jaddada cewa an goge wasu sassa na hirar don ba cikakkiya ba ce.

Leave a Reply