Home Labaru Sojojin Sama Sun Lalata Wata Cibiyar ‘Yan Ta’adda

Sojojin Sama Sun Lalata Wata Cibiyar ‘Yan Ta’adda

768
0

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar tarwatsa wata cibiyar sufuri ta mayakan kungiyar Boko Haram dake Bula-Bello a jihar Borno.

Darektan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar Ibikunle Daramola, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce atisayen ‘Green Sweep 3′ da dakaru na musamman ke gudanar wa a karkashin babban atisayen ‘Lafiya Dole’ na taimakawa a nasarorin da rundunar soji ke samu a yakin da take yi da kungiyar .

Daramola, ya ce daga cikin irin hare-haren da dakarun ke kai wa ne suka sami nasarar rushe wata cibiyar sufuri ta mayakan kungiyar Boko Haram dake yankin Bula Bello mai makwabtaka da dajin Sambisa.

Daramola, ya bayyana cewa dakarun rundunar sun kai hari cibiyar ne bayan samun bayanan sirri da kuma yin amfani da jiragen yaki na musamman domin tabbatar da cewa kungiyar ta Boko Haram na amfani da cibiyar domin shirya  da kaddamar da hare-hare a kan rundunar sojoji.

Ya kara da cewa dakarun sun kai hari cibiyar ne ta hanyar yin amfani da wasu jiragen yaki guda biyu samfurin ‘Alpha Jets’ da kuma wani jirgin yaki mai saukar ungulu samfurin Mi-35M.

Daramola ya ce saida dakarun sojin suka tabbatar da motsin kungiyar Boko Haram a cibiyar ta hanyar amfani da na’urorin cikin jirginsu na yaki kafin su fara luguden wuta a cibiyar.