Home Labaru Gwamnati Ta Kafa Kwamitin Bincike Da Zai Kwato Naira Biliyan 614 Daga...

Gwamnati Ta Kafa Kwamitin Bincike Da Zai Kwato Naira Biliyan 614 Daga Jihohi

238
0
Zainab Shamsu Ahmad, Ministar kudi Ta Najeriya
Zainab Shamsu Ahmad, Ministar kudi Ta Najeriya

Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamitin bincike da zai bi sawun wasu makudan kudaden bashi da gwamnatocin jahohi 35 suka ciyo daga gwamnatin tarayya da sunan tallafin kasafin kudi.

Ministar kudi ta Najeriya , Zainab Shamsu Ahmad ce ta bayyana haka ga manema labarai, bayan kammala taron majalisar tattalin arzikin kasa wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a Abuja.

Ministar ta ce kowace jiha daga cikin jahohin 35 za ta biya naira biliyan 17 da milliyan 5,  saboda haka majalisar ta amince da kafa kwamiti daya kunshi kungiyar gwamnoni da ma’aikatar kudi, da kuma babban bankin Najeriya CBN domin fitar da tsarin biyan kudaden.

Daga karshe ministar ta nanata muhimmanci karkata akalar tattalin arzikin Najeriya daga man fetir zuwa wasu harkoki da za su kara mata adadin kudaden shiga, domin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi ga matasa a wa’adin mulkinsa na biyu.