Home Labaru Ilimi Gwamnati Ta Kashe Naira Tiriliyan 1 A Kan Ilimi – Buhari

Gwamnati Ta Kashe Naira Tiriliyan 1 A Kan Ilimi – Buhari

198
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta kashe naira tiriliyan 1 da billiyan 3 wajen inganta harkokin ilmi daga shekarar 2015 zuwa yau a Najeriya .

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da cibiyar ilmin difloma, wadda babban bankin Najeriya (CBN) ya gina a Jami’ar Ahmadu Bello, dake Zariya.

A wata sanarwa da mai  magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar, ya ce Buhari ya yi amfani da damar ya sake jaddada kokarin da gwamnatinsa ke yi, domin ganin ta samar da ingantaccen ilmi ga ‘yan Najeriya.

Shugaban kasa ya ce cibiyar za ta kara bijiro da kyawawan ayyukan hangen-nesan da marigayi Sir Ahmadu Bello ya samar ta kai ga ya kafa jami’ar shekaru 60 da suka gabata.

Ya kara tunatar da irin gudumawar da Jami’ar Ahmadu Bello ta bayar wajen ci gaban Najeriya baki daya, inda ya ce babu shakka wannan zai sa ba za a taba mantawa da gagarumar gudummawar da Sardauna ya bayar ba.