Home Labaru Sojojin Ruwan Maroko Sun Ceto Baƙin Haure Ƴan Afirka 141

Sojojin Ruwan Maroko Sun Ceto Baƙin Haure Ƴan Afirka 141

140
0

Sojojin ruwan Maroko sun ceto bakin haure 141 ‘yan Afirka da ke cikin wani kwale-kwale da ya matsala a lokacin da suke tafiya daga Mauritania zuwa tsibirin Canary na kasar Spain.

An ceto mutanen ne a ranar Lahadi, kimanin kilomita 274 kudu maso yammacin Dakhla a cikin hamadar yammacin sahara.

Baƙin hauren dai, sun tashi ne daga gabar tekun Mauritaniya a ranar 10 ga watan Fabrairu, kamar yadda rahotanni daga sojojin ruwan Morocco suka ruwaito.

Idan ba a manta ba, a bara tsibirin Canary ya karƙi kusan baƙin haure dubu 32, wanda ya zama mafi yawan adadin da aka samu tun shekara ta 2006.

Haka kuma, a watan Janairu hukumomin Spain sun bada rahoton ci gaba da ƙaruwar bakin haure zuwa tsibiran, inda aƙasarin jiragen ruwan suna fito wa ne daga Mauritania.

Leave a Reply