Home Home Tashin Hankali Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Farmaki Hedikwatar ‘Yan Sanda A...

Tashin Hankali Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Farmaki Hedikwatar ‘Yan Sanda A Zamfara,

129
0

Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari a shelkwatar rundunar ‘yan sanda da ke garin Zurmia ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Wata majiya ta ce, ‘yan ta’addan sun mamaye garin ne a ranar Lahadi 18 ga watan Fabrairu, inda suka kashe mutane bakwai ciki har da ɗan sanda ɗaya.

Wani mazaunin garin mai suna Babangida Zurmi ya ce har yanzu bai yi magana da wani ɗan uwansa ba, saboda yawancin lambobinsu a kashe suke.

Majiyar ta kuma bayyana cewa, ‘yan bindigan sun kai hari garin ne domin ɗaukar fansa a kan kisan da wasu ‘yan banga suka yi wa abokan aikinsu biyu.

Babangida ya ce miyagun sun kuma ƙona shaguna da dama sannan suka ƙona shelkwatar ‘yan sanda da ke Zurmi, sai dai kawo yanzu babu wani rahoto a kan faruwar lamarin da jami’an ‘yan sanda

Leave a Reply