Home Home Kamfanin AEDC Ya Yi Barazanar Yanke Wa Fadar Shugaban Najeriya Wutar Lantarki

Kamfanin AEDC Ya Yi Barazanar Yanke Wa Fadar Shugaban Najeriya Wutar Lantarki

97
0

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja AEDC ya yi barazanar katse wutar lantarki a fadar shugaban Nijeriya da na wasu ma’aikatun Gwamnatin Taryya 86 a kan bashin kuɗin wuta na sama da naira biliyan 47 da ya ke bin su.

Wasu daga cikin ma’aikatun da barazanar ta shafa sun haɗa da ma’aikatar kuɗi da ta yaɗa labarai da ta kasafin kuɗi da ta ayyuka da gidaje, da gwamnan CBN da ofishin Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, da sauran su.

A cikin sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Litinin, kamfanin ya bai wa ma’aikatu da ofisoshin na gwamnati wa’adin kwanaki 10 domin biyan basukan ko kuma a yanke musu lantarki, wato tun daga 28 ga watan Fabarairun shekarar nan.

Bangaren samar da wutar lantarki a Nijeriya dai ya shafe shekaru yana fama da matsalar bashi.

A makon da ya gabata ne Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce umarci kamfanonin rarraba wutar lantarki DisCos da su tashi tsaye idan ba haka ba duk wanda a ka samu da laifi, za a soke lasisin sa.

Leave a Reply