Home Labaru Babu Gaskiya A Batun Cewa Ana Binciken Ofishin Abba Kyari — Garba...

Babu Gaskiya A Batun Cewa Ana Binciken Ofishin Abba Kyari — Garba Shehu

428
0
Babu Gaskiya A Batun Cewa Ana Binciken Ofishin Abba Kyari --Garba Shehu
Babu Gaskiya A Batun Cewa Ana Binciken Ofishin Abba Kyari --Garba Shehu

Fadar shugaban kasa ta maida martani bisa rahotannin da ke cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ragamar mulkin sa ga marigayi Abba Kyari.

Garba Shehu

A wani jawabi da babban mai Magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya gabatar, ya ce shugaba Buhari ne al’ummar Nijeriya su ka zaba, kuma shine mai wuka da nama, ba wani ba.

Garba Shehu ya kuma karyata rade-radin cewa, shugaban kasa Buhari ya bada umarni soke duk wasu mukamai da Abba Kyari ya bada daf da kwanciyar sa jinya.

Martanin dai na zuwa ne sakamakon yadda rahotanni a kafafen yada labarai cewa, shugaban kasa Buhari ya soke wasu takardu da tsohon shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa ya sa hannu a kai, zancen Malam Garba Shehu ya karyata.

Leave a Reply