Home Labarai Sojojin Nijeriya Sun Kashe Wasu Mayakan Kungiyar IPOB

Sojojin Nijeriya Sun Kashe Wasu Mayakan Kungiyar IPOB

67
0

Rundunar sojojin Nijeriya, ta ce dakarun ta sun kashe wasu ‘yan kungiyar IPOB biyu a wani ba-ta-kashi da su ka yi.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafin ta na
Tuwita, ta ce dakarun ta sun kuma kama ‘yan kungiyar IPOB
hudu a Orlu da ke jihar Imo.

Sanarwar ta kara da cewa, binciken da aka gudanar a wayoyin
salula na mutanen, ya nuna hotuna da bidiyon mutanen da aka
kashe a wuraren bauta na gargajiya.

Rundunar sojin ta cigaba da cewa, an gano bindigogi da sauran
miyagun abubuwa a hannun mutanen.