Rahotanni na cewa, gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da tsarin ‘Babu Aiki – Babu albashi a kan malaman jami’o’in da ke yajin aiki.
Idan dai ba a manta ba, kungiyar malaman jami’o’i ASUU, ta
tsunduma yajin aikin makonni hudu a ranar 14 ga watan
Fabrairu sannan ta sabun ta bayan ya kare.
Shugaban kungiyar kwalejojin kimiyya da fasa na kasa
Kwamred Ibeji Nwokoma, ya tabbatar cewa ba a biya ‘yan
kungiyar albashin su na watan Maris ba.
Sai dai Mista Nwokoma ya ce, wannan matakin da gwamnatin
tarayya ta dauka ba zai hana su neman hakkokin su ba.