Home Labarai Majalisar Dattawa Na Da Hurumin Bincikar Shugaban Kotun Da’ar Ma’aikata – Kotu

Majalisar Dattawa Na Da Hurumin Bincikar Shugaban Kotun Da’ar Ma’aikata – Kotu

27
0

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta ce Majalisar Dattawa na da hurumin binciken shugaban Kotun Da’ar Ma’aikata Danladi Umar, bisa zargin cin zarafin wani mai gadi a wata kasuwa da ke unguwar Wuse a Abuja.

Da ya ke yanke hukunci, mai shari’a Inyang Ekwo ya ce
shugaban kotun CCT ya kasa nuna kyawawan dabi’u na
mu’amala da jama’a ta hanyar halayen sa, la’akari da cewa
hukumar Da’ar Ma’aikata ta ginu ne a kan wata doka da
Majalisar Dokoki ta kasa ta amince da ita, don haka ta na da
hurumin binciken halinsa.

Daga bisani kotun ta yi watsi da bukatar da Umar ya shigar, inda
ke neman a dakatar da binciken da kwamitin kula da yanayin
da’a na Majalisar Dattawa saboda rashin cancantar bukatar.

Shugaban Kotun Da’ar Ma’aikata Danladi Umar dai, ya na
kalubalantar ikon Majalisar Dattawa na gudanar da bincike a
kan sa, bisa zargin da ake yi ma shi na cin zarrafin wani mai
gadi a kasuwar Banex da ke Abuja.