sojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 624, sun kuma kama 1,051, sannan sun ceto mutum 563 a watan Mayun nan da muke ciki.
Daraktan yada labarai na shelkwatar tsaron, Manjo Janar Edward Buba ne, ya bayyana hakan ga ‘yan jarida a nan Abuja.
yi kira ga ‘yan Nijeriya su kasance masu goyon bayan sojoji wajen yaki da ta’addanci da ‘yan fashi da sauran masu aikata laifuka.
Janar Buba ya sake nanata cewa al’ummar kasa na da irin rawar da za su taka wajen kawo karshen hare-haren ta’addancin.
Ya ce dakarun sun kwato makamai guda 707, sun kuma gano bindigogi kirar AK-47 guda 411 da kananan bindigogi guda 234 da sauran .
Manjo Janar Buba ya ce ragowar kayayyakin da aka kawto na sata sun hada da litar mai 4,871,470 da danyen mai lita 931,416.














































