Dakarun runduna ta ɗaya ta sojin Najeriya sun kashe wasu ‘yan bindiga shida
tare da kama wasu mutum uku a wani samame na musamman a ƙaramar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna Samuel Aruwan,
ya ce sojojin sun samu nasarar kakkaɓe ‘yan bindigar ne bayan samun bayanan sirri a yankin Galadimawa karamar hukumar Giwa.
Ya ce sojojin sun kwato wasu shanu suka miƙa su ga mutanen yankin daga nan ne suka hango maharan a kasuwar Galadimawa,
inda aka yi musayar wuta takanin ɓangarorin biyu, kafin daga bisani maharan suka arce bayan kisan mutum shida daga cikinsu.
Samuel Aruwan, ya ce bayan ƙaddamar da bincike a yankin ne kuma sojojin suka kama wasu mutum uku da ake zargi da hada baki tare,
Sojojin sun kuma samu nasarar ƙwato babura biyu tare da wayoyin hannu huɗu a lokacin gumurzun.