Home Labaru Sojoji Sun Gano Gawarwakin Mutane A Sansanonin Kungiyar IPOB

Sojoji Sun Gano Gawarwakin Mutane A Sansanonin Kungiyar IPOB

114
0

Rundunar Sojin Nijeriya, ta ce ta gano gawarwakin mutane a sansanonin haramtacciyar kungiyar ‘yan a-waren Biafra ta IPOB yayin da su ka kai samame a kan su.

Mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya ce gawarwakin na mutanen da mayakan su ka yi garkuwa da su ne, a kananan hukumomin Ihiala da Orsulu da ke Jihohin Anambra da Imo.

Janar Nwachukwu, ya ce dakarun soji sun yi nasara a kan mayakan ta hanyar yi ma su kwanton-bauna, lamarin da ya ba su damar gano gawarwakin da tuni sun fara lalacewa.

Kakakin sojin, yace sun yi nasarar tarwatsa irin wadannan sansanonin guda 4, a kan hanyar Orsumoghu zu Mbosi da Ihiala zuwa Uli da ‘yan haramcaciyar kungiyar su ka kafa.

Janar Nwachukwu ya ce dakarun soji sun hallaka mutum guda tare da kama wasu mutane uku, yayin da su ka gano bindigogi da harsasai da wayoyin salula guda biyu da mota kirar Hilux da tabar wiwi da kuma kudi, wadanda ya ce tuni an an mika su ga Rundunar Yan Sanda ta Jihar Enugu.