Home Labaru Dakarun Nijeriya Sun Kashe ‘Yan Bindiga 55 A Kaduna

Dakarun Nijeriya Sun Kashe ‘Yan Bindiga 55 A Kaduna

117
0

Dakarun rundunar Operation Thunder Strike da Whirl Punch, sun kashe ‘yan bindiga 55 a yankin Labi da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Daraktan yada labarai na ma’aikatar tsaron Nijeriya Manjo Janar Benard Onyeuko ya bayyana wa manema labarai haka a Abuja, inda ya ce mayakan rundunar sun yi wa ‘yan bindigr dirar mikiya ta sama ne yayin fafatawar, inda su ka rika yi wa ‘yan bindigar ruwan alburusai.

‘Yan bindiga dai sun addabi al’umar yankuna da dama a yankin arewa maso yammacin Nijeriya, inda su ke satar dabbobi da kuma mutane domin karbar kudin fansa.

A cikin wannan makon, gwamnatin taraya da na jihohi sun bayyana shirin hada karfi da karfe wajen yakar ‘yan bindigar da ke cin zarafin al’umma.