Home Labaru Gwamnati Za Ta Karasa Manyan Ayyukan Da Ta Fara Kafin Buhari Ya...

Gwamnati Za Ta Karasa Manyan Ayyukan Da Ta Fara Kafin Buhari Ya Sauka – Minista

87
0

Ministan ayyuka Babatunde Fashola, ya ce za a kammala titin Abuja zuwa Kano da na Legas zuwa Ibadan da gadar Neja nan da watanni 12 masu zuwa.

Fashola ya bayyana haka ne, a wajen wani taron jin ra’ayoyin jama’a da ya gudana a Abuja, wanda Ma’aikatar yada labarai da raya al’adu ta saba yi domin bayyana irin nasarorin da gwamnati ta samu.

Ministan, ya ce ma’aikatar sa ta bada kwangilolin tituna dubu 1, da 18 na ayyuka 859 a jihohi 36 da garin Abuja.

Ya ce gwamnatin tarayya za ta yi kokari domin ganin ta kammala duk wadannan manyan ayyukan kafin wa’adin mulkin shugaba Buhari ya cika.