Home Labaru Sojin Ruwan Najeriya Sun Kama Wani Jirgin Ruwa Dauke Da Kilo 32...

Sojin Ruwan Najeriya Sun Kama Wani Jirgin Ruwa Dauke Da Kilo 32 Na Hodar Koken

14
0

 

Jami’an rundunar sojin ruwan Najeriya na BEECROFT, sun ce sun kama kilo 32  na hodar koken a cikin wani jirgin ruwa, samfurion MV Chayanee Naree.

Rundunar ta ce an kama jirgin ruwan da ma’aikatan sa mutum shida waɗanda duk ƴan yankin nahiyar Asiya ne.

Rahotanni sun ce an sanya koken din a cikin wata jaka aka ɓoye a wajen saka kaya na jirgin ruwan, wanda ya taso daga Brazil.

Kwamandan BEECROFT Commodore Bashir Mohammed, ya ce an samu nasarar kama kayan ne saboda hadin kai da aka samu tsakanin rundunar soji da hukumar ƴan sanda ta ƙasa da ƙasa da hukumar kwastam ta Najeriya da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma hukumar tashar jiragen ruwan Najeriya.

Ya ce an hango jirgin ruwan tun daga nisan kilomita 250 a gabar tekun Jamhuriyyar Benin ranar 1 ga watan Oktoban 2021 inda yake tangal-tangal kusan mako ɗaya kafin daga baya ya taho gadan-gadan cikin ruwan Najeriya.