Home Labaru Sama Da ‘Yan Ta’Adda Dubu 13 Da Iyalan Su Sun Mika Wuya...

Sama Da ‘Yan Ta’Adda Dubu 13 Da Iyalan Su Sun Mika Wuya A Jihar Barno

27
0

Shelkwatar tsaro ta kasa ta bayyana cewa zuwa yanzu ‘yan ta’adda dubu 13 da 243 da iyalen su ne suka mika wuya a Arewa Maso Gabas.

Mataimakin shugaban yada labarai na rundunar Bernard Onyeuko ya sanar da haka a nan Abuja ranar Alhamis inda yake bayyana nasarorin da rundunar ta samu a fadin Najeriya.

Onyeuko, ya ce daga cikin tubabbun akwai maza dubu 3 da 343, mata dubu 3 da 868 da yara kananan dubu 6 da 234.

Ya ce rundunar Operation Hadin kai ta samu wannan nasara a cikin makonni biyu ne saboda luguden wuta babu kakkautawa da ta sama da ƙasa da suka rika yi.

Onyeuko, ya ce aman wuta da aka rika yi wa maharan ta sama da ƙasa a wurare daban daban a yankin Arewa maso Gabas ya taimaka wajen tarwatsa maharan da kama wasu daga cikin su inda a ciki akwai masu kawo wa Boko Haram bayani game da gari da masu siyar musu da kaya.