Home Labaru Matsayar Newcatle A Ingila

Matsayar Newcatle A Ingila

142
0

Rahotanni sun ce ba sabon labari ba ne cewa Kamfanin Public Investmen Fund na Saudiyya da aka kiyasta ya mallaki fam biliyan 700 ya sayi kashi 80 na kulob din Newcastle akan fam miliyan 305, wanda ya sa kulob din ya zama daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafa mafiya arziki a duniya a dare daya.

Kusan an kulla wannan ciniki ne a lokacin da ake hutu a gasar firimiya saboda haka da dama sun kagu suga yadda abubuwa za su sauya a Newcastle kafin a bude kasuwar cinikin yan wasa a watan Janairu.

Wato a yanzu Newcastle na na 19 a teburin firimiya, saboda haka masana ke fadin cewa dole ne a watan Janairu su yi irin dabarar da Manchester City ta yi a 2009, da ta kawo Carlos Tevez wanda yasa manyan yan wasa suma suka ji cewa za su iya zuwa kungiyar.

Leave a Reply