Home Labaru Soji Sun Yi Luguden Wuta A Dajin Birnin Gwari Dake Jihar Kaduna

Soji Sun Yi Luguden Wuta A Dajin Birnin Gwari Dake Jihar Kaduna

41
0

Shelkwatar tsaro ta Nijeriya ta ce jiragen yaki sun yi luguden bama-bamai a dajin Kwaga cikin yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna inda suka kashe akalla ‘yan fashin daji 40.

Shelkwatar ta kuma ce a yayin hare-haren ta sama an lalata maboya da sansanonin ‘yan fashin da dama a jihar Kaduna da Katsina da kuma Sokoto.

Kazalika an kuma kama wasu gaggan ‘yan fashin daji da suka yi kaurin suna a Dajin Dangulbi na jihar Zamfara.

Shelkwatar tsaron ta ce Cikin ‘yan fashin dajin da kuma masu tsegunta musu bayanai da ke cikin jerin wad’anda jami’an tsaro ke nema kuma, daga farkon watan Oktoba na 2021 zuwa tsakiyar sa, dakarunta sun kama Mamuda Aliyu Dangulbi, da Rilwan Sani Dangulbi, da Yusuf Adamu Dangulbi, da kuma Yakubu Umar Maihaja, dukkan su a yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Ta ce a yayin hare-haren na jami’an tsaro an kuma kubutar da fararen hula da aka sace tare da gano makamai da alburusai da dama.