Home Labaru Kiwon Lafiya Gwamnatin Kano Za Ta Kula Da Masu Fama Da Ciwon Ido Kyauta

Gwamnatin Kano Za Ta Kula Da Masu Fama Da Ciwon Ido Kyauta

11
0

Masu larurar idanu dubu 14 ne za su amfana da aikin duba idanu da bada magani da samar da gilashi kyauta a Jihar Kano.

Kwamishinan ma’aikatar lafiya na Jihar Kano, Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya bayyana haka a yayin hira da manema labarai a kan zagayowar ranar gani ta duniya a dakin taro na ma’aikatar lafiya.

Ya ce, ranar idanu ta duniya ana yi ne a duk ranar Alhamis ta biyu ta watan Oktobar kowace shekara kuma duba masu larurar zai gudana ne a dukkan masarautu biyar na jihar.

Ya ce, taken shirin na wannan shekarar shi ne Muso Idanuwammu,

Kwamishinan ya kara da cewa alkaluma sun nuna kashi 90 na larurar idanu ana samu ne a kasashen Afirka, mafi yawanci kuma yafi shafar mata, Larura ce kuma da za a iya kare kai daga kamuwa wadanda suka kamu kuma za a iya magance ta.

Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya ce Jihar Kano ta fara shig bikin wannan rana ce tun shekarar 2019 an kuma yi wa masu larurar dubu 16 magani kyauta.

Ya ce, yanzu haka Gwamnatin jiahr Kano karkashin jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta sanya kayan aikin kula da lafiyar idanu a asibitoci da ba ma’aikata horo don rage larurar idanu.