Home Labaru Sojan-Gona: Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kama Jami’in Hukumar EFCC Na Bogi

Sojan-Gona: Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kama Jami’in Hukumar EFCC Na Bogi

196
0

Jami’an ‘yan sanda a jihar Legas, sun kama wani mutum mai shekaru 29 mai suna Emeka Emmanuel bisa zargin sa da sojan-gona a matsayin jami’in hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar Bala Elkana, ya ce an kama wanda ake zargin da laifin damfarar mutane ta hanyar yi masu alkwarin sama masu aiki a hukumar EFCC a matsayin sa na jami’in ta.

Wanda ake zargin dai ya mallaki katin bogi na shaidar zama jami’in hukumar EFCC, wanda ya ke amfani da shi wajen damfarar mutane.

Bayan damfara, an kuma kama Emeka da laifin mallakar cibiyar lafiya a gidan sa, sannan sauran abubuwan da aka samu a gidan sa sun hada da kayayyakin kiwon lafiya da shaidun karatu na bogi.