Home Labaru Takaddama: Kotu Ta Aika Wa Rochas Okorocha Sammaci Bisa Zargin Take Doka

Takaddama: Kotu Ta Aika Wa Rochas Okorocha Sammaci Bisa Zargin Take Doka

240
0
Rochas Okorocha, Tsohon Gwamnan Jihar Imo
Rochas Okorocha, Tsohon Gwamnan Jihar Imo

Wata kotun Majistare da ke birnin Owerri na jihar Imo, ta aika wa tsohon gwamnan jihar Rochas Okorocha sammaci bisa zargin furta kalaman kiyayya.

Rochas Okorocha zai bayyana a kotu ranar 8 ga watan Oktoba, bayan gwamnatin jihar Imo ta yi karar shi bisa zargin cewa ya  na ingiza magoya bayan shi wajen bijire wa gwamnati.

Babban Lauyan jihar Imo ya yi zargin cewa, Okorocha ya kasance da dabi’ar yin kalaman da ka iya ingiza magoya bayan sa a kan gwamnati, ta hanyar yin amfani da gidan radiyon sa na Reach FM.

Lauyan, ya kuma yi zargin cewa, Okorocha ya na shafe tsawon lokaci a birnin Owerri, tare da yin amfani da ‘yan bangar siyasa da aka fi sani da ‘Ohaji Boys’, wadanda ya dauka aiki domin tada zaune tsaye.

Gwamnatin jihar Imo ta yi zargin cewa, wani hadimin Gwamna Emeka Ihedioha ya sha duka, yayin da ya ke kan gudanar da aikin tsare-tsaren kotu a kan lamarin da ya shafi gidan Okorocha.